Nazarin da jaridun kasar Jamus suka yi kan muhimman batutuwan da suka wakana a nahiyar Afirka. | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 25.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Nazarin da jaridun kasar Jamus suka yi kan muhimman batutuwan da suka wakana a nahiyar Afirka.

Zaben gama gari da aka gudanar a kasar Angola da ya kawo karshen mulkin kimanin shekaru 38 na Jose Eduardo dos Santos ya dauki hankalin jaridun Jamus a wannan mako.

Karshen mulkin dos Santos a kasar Angola

Tabbas zai sauka a wannan karo, inji jaridar Berliner Zeitung a labarin da ta buga game da zaben na kasar Angola tana mai cewa 'yan Angola sun zabi mutumin da zai maye gurbin Shugaba dos Santos. Ta ce tun wasu watanni da suka wuce zaben kasar ta Angola da aka gudanar a wannan Laraba ya dauki hankalin duniya. Ta ce a farkon shekara shugaban kasa Jose dos Santos mai shekaru 74 wanda kuma ya shugabanci kasar tsawon shekaru 38 ya ba da sanarwar cewa ba zai sake tsayawa takara ba, kuma abin mamaki da gaske shugaban yake. Watakila saboda cutar daji wato cancer da yake fama da ita ta tilasta shi daukar wannan mataki. Kasarsa na neman wani shugaba sabon jini da zai farfado da tattalin arzikinta da ke fama da masassara. Sai dai jam'iyyarsa ta MPLA ce za ta ci gaba da rike madafun iko karkashin dan takararta kuma tsohon ministan tsaro Joao Lourenco.

Zanga-zangar nuna kyama da mulkin mulaka'u a kasar Togo

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung a wannan makon ta leka kasar Togo inda a karshen mako aka gudanar da zanga-zangar adawa da mulkin 'yan gidan Gnassingbe Eyadema. Ta ce akalla mutane biyu aka kashe sannan wasu 13 suka samu raunika a zangar-zangar da aka gudanar a Lome babban birnin kasar da kuma wasu garuruwa na kasar. Sai dai 'yan adawa sun ce yawan wadanda aka kashe a lokacin da 'yan sanda suka yi amfani da karfi fiye da kima a kan masu zanga-zangar ya kai mutum bakwai. Jaridar ta ce boren da aka yi wa taken shekaru 50 sun yi yawa, bai kai ga samun cikakken hadin kan 'yan adawa a kasar ba wadda tun kimanin shekaru 50 ke nan take karkashin shugabancin 'yan gidan Gnassingbe.

Zargin da aka yi wa madam Mugabe 

A karshe sai jaridar Neue Zürcher Zeitung da ta yi tsokaci kan rigar kariya da Grace Mugabe uwargidan shugaban Zimbabuwe Robert Mugabe ta samu a Afirka ta Kudu bayan ta doki wata matashiya har ta yi mata rauni a wani otel, bayan ta ganta tare da danta a otel din. Grace Mugabe dai ta samu rigar kariya ta diplomasiyya abin da ya hana a gurfanar da ita gaban kotu bayan cin zarafin matashiyar 'yar shekaru 20 da haihuwa.