1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Navalnaya: Duniya na bukatar tashi tsaye a kan Putin

Abdullahi Tanko Bala
February 28, 2024

A wani jawabi mai ratsa zukata Yulia Navalnaya uwar gidan jagoran adawar Rasha Alexei Navalny ta shaida wa majalisar dokokin Turai cewa lokaci ya yi da duniya za ta tashi tsaye a kan shugaban Rasha Vladimir Putin

https://p.dw.com/p/4d08H
Julia Navalnaya a majalisar dokokin Turai
Hoto: Johanna Geron/REUTERS

Yulia Navalnaya uwar gidan marigayi jagoran adawar Rasha Alexei Navalny ta gabatar da jawabi a zauren majalisar dokokin Turai da ke Strasbourg a Faransa 

Da ta ke jawabiNavalnaya ta baiyana Starsbourg a matsayin daya daga cikin biranen da Navalny ya ke kauna tare da tunato da ziyarar da suka kai da magidanta da yayansu shekaru uku da suka wuce, ta ce sai dai a yau ta dawo ba tare da iyalinta ba.

Yulia Navalnaya ta ce lokaci ya yi da duniya za ta tashi tsaye a kan shugaban Rasha Vladimir Putin da mutanen da ke kewaye da shi tare da karfafa wa yan adawa domin gina kyakkyawar makoma ga Rasha. 

Yan majalisar dokokin Turan sun kuma yi muhawara a kan kisan jagoran adawar Alexei Navalny tare da yin kakkausar suka kan gwamnatin Rasha da shugaba Vladimir Putin .

Yan majalisar sun nuna damuwa kan mummunan halin da yan adawa da yan jarida da masu kare hakkin bil Adama suke ciki a Rasha.