1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban kasa mai ci ya fadi a zaben Malawi

June 28, 2020

Ana ci gaba da murna da shagulgulan lashe zabe a Malawi bayan a yammacin Asabar an bayyana madugun adawa a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/3eRtz
Malawi Opposition Lazarus Chakwera
Shugaban kasar Malawi (mai jiran gado) Lazarus Chakwera Hoto: Reuters/E, Chagara

Lazarus Chakwera mai shekaru 65 ya samu kaso 58 na kuru'un da aka kada, abin da ya ba shi damar kayar da  shugaba mai ci Peter Mutharika. 

A watanni goma sha uku da suka wuce aka bayyana cewa Peter Mutharika wanda ke mulki tun shekara ta 2014 a matsayin wanda ya lashe zabe a karo na biyu. Sai dai a farkon shekarar nan kotu ta soke zaben, ta umarci a sake fafatawa. To amma a yanzu da aka bayyana cewa Mutharika ya fadi zabe, shugaban ya nuna bacin ransa. 

''Mu fa a matsayinmu na kasa muna cike da mamaki, wai wannan sahihin zabe ne kuwa? Ina ba 'yan kasar nan shawara su kama jimamin abin da ya faru. Ina kira ga 'yan Malawi su ci gaba da harkokinsu cikin nutsuwa.'' inji Shugaba Mutharika.