NASA na sa ran samun halittu masu rai a duniyar Mars | Labarai | DW | 29.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

NASA na sa ran samun halittu masu rai a duniyar Mars

Hukumar binciken sararin samaniya ta Amirka wato NASA ta ce ta akwai yiwuwar a samu halittu masu rai a duniyar Mars bayan da aka gano ruwan a cikinta

Hukumar binciken sararin samaniya ta Amirka wato NASA ta ce ta samun kwarin guywar yiwuwar samun halittu masu rai a cikin duniyar Mars bayan da binciken da ta gudanar a baya bayan nan ya gano ruwa a cikinta. John Grunsfeld, mataimakin shugaban wannan hukuma ne ya sanar da hakan a jiya Litani inda ya ce a yanzu kam sun samu dama ta zuwa guraren da suke kyautata samun halitta mai ray a cikin duniya ta Mars.

Sannan ya ci gaba da cewa yana fatan labari wannan na ci gaba da aka samu zai kara karfafa masu binciken kimiya ga gaggauta kirkiro da na'urori da za su iya gano halittu a cikin wannan duniya ta Mars da ake yiwa lakabin jar duniya.

Hukumar ta NASA ta ce tuni ma dai ta kera wata na'ura mai suna Insight za ta aika da ita a shekara 2016 domin gudanar a karo na farko da bincike a karkashin kasar duniyar ta Mars domin gano ruwan da suke kyautata ta kunsa da kuma ka iya kasancewa wata sabuwar damar gudanar da ayyukan noma kiwo da dai sauransu a shekaru masu zuwa.