Napoli za ta hana ′yan wasanta zuwa AFCON | Labarai | DW | 03.08.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Napoli za ta hana 'yan wasanta zuwa AFCON

A yayin da yake magana da 'yan jarida a Italiya, mai kulob din Napoli ,Aurelio De Laurentiis ya ce ya lura cewa a duk lokacin da aka zo gasar AFCON ba ya samun hankalin 'yan wasansa na Afirka.

Mamallakin kungiyar kwallon kafar Napoli ta kasar Italiya Aurelio De Laurentiis ya ce daga yanzu ba zai sanya hannu a kan kwantaragi da wani dan kwallo na Afirka ba har sai dan wasan ya amince a rubuce cewa ba zai shiga gasar kwallon kafar Afirka ta AFCON ba. 

Dan wasan Senegal Kalidou Koulibaly wanda yanzu ke a kungiyar Chelsea da dan Kamaru Andre Zambo Anguissa na cikin 'yan wasan Afirka da suka rasa wasannin kungiyar Napolin a farkon shekarar nan a sakamakon wakiltar kasashensu da suka yi a gasar kwallon kafar Afirka ta AFCON.