Nakiya ta hallaka fararen hula a Mali | Labarai | DW | 31.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nakiya ta hallaka fararen hula a Mali

Ba a bayyana yawan mutane da tashin nakiya ya yi awan gaba da rayukansu ba a arewacin Mali. Amma kuma wani harin kunar bakin wake ya jikata wani soja a wannan yanki.

Wani dan kunar bakin wake da ya tayar da bam ya jikata wani soja a garin Timbuktu na arewacin kasar Mali.Jami'ai sun ce cikin wani lamarin na daban tashin nakiya da a ka binne, ya hallaka wasu fararen hula uku. Wannan na faruwa ne lokacin da Shugaban Faransa Francois Hollande ya bayyana cewa an cimma muradun da a ka saka a gaba a arewacin Mali, sannan za a fara janye dakarun kasar na ba da dadewa ba.

Dakarun na Faransa sun taimaka wajen sake kwato yankin arewacin kasar ta Mali daga hanun 'yan tawaye masu alaka da kungiyar al-Qaeda.Ita dau Mali ta fada hannun masu kaifin kishin addinin Islama bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin Toumani Toure.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe