Najeriya ta sanar da ranara jigilar alhazai
August 22, 2013Gwamantin Najeriyar ta sanar da matakan aikin Hajjin bana saboda kaucewa abinda ya faru a bara. Yanzu dai a ranar 14 ga watan Satumba mai zuwa aka ajiye a matsayin ranar da za'a fara jigilar mahajjatan kasar zuwa Saudiyya.
Sanar da ranar da za'a fara jigilar mahajattan Najeriyar zuwa kasar ta Saudiyya dai, muhimmin mataki ne a shirye-shiryen da aka dade ana yi domin gagarumi kuma muhimmin aikin jigilar mahajattan kasar da a duk shekara ke zama aiki da ke ciki da kalubale.
Sanin irin matslalolin da Najeriyar ta fuskanta a shekarar da ta gabata inda rashin muharami ga mata mahajatta ya haifar da matsalolin, da ya sanya maido da wasu da dama a bana hukumar tace dole ne ko wace mace ta kasance da muharamminta. To sai dai duk da fara shiri da wuri akan fuskanci matsaloli na jinkiri da ma zargin kamfanonin da aka baiwa aikin gaza kulawa da bukatun mahajattan, ba tare da ganin zahirin hukuncin da aka yi masu. Malam Muhammad Musa Bello shugaban hukumar aikin hajjin Najeriyar yace a bana kam ba sani ba sabo.
"Abinda muka shaida masu shine dole ne kowa ya tsaya ya yi aiki tsakaninsa da Allah, an san wannan harka ce ta kasuwanci, amma kada su manta cewa duk fasinjan da suke dauka za su je kasar Sa'udiyya ne, domin wata ibada da ke da muhimmanci a addinin Islama. Don haka su tabbatar da sun cika alkawarin da suka yi wa kowane Alhaji, kuma duk kamfanin da ya saba alkawari to za'a hukunta shi. Abinda ya faru bara ya riga ya faru, kuma ba zai sake faruwa ba domin an dauki matakai a kan hakan''
A yayinda kalilan daga cikin mahajattan Najeriyar da suka samu nasarar shiga cikin jerin wadanda ke sa ran sauke farali a wanan shekarar, mahajatta da dama suna ci gaba da nuna damuwa a kan yadda ake tafiyar da aikin, musamman jigilar da akan baiwa kamfanonin jiragen sama. Alhaji Abubakar Ibrahim ya dade yana aikin hajji a Najeriya, kuma ya bayyana irin abubuwan da suka fuskanta.
"Maganar aikin hajji a Najeriya kullum za ka ji shugabanni su ce an gyara an gyara, amma maganar dai tana nan guda ce, za'a yi kokarin jigilar mahajatta a kan lokaci, amma wajen dawowa sai a yi ta sa maku rana, amma sai a kai sati biyu ba'a kwasheku ba, karshe lokacin da za'a zo a daukeka alhaji ya kashe kudinsa, abinci ma a wahalce yake samunsu.''
Wanan ya sanya na tauntubi Alhaji Ibrahim Dahiru jami'in yada labaru na Max Air, wanda shine kamfanin da ya fi jigilar mahajattan masu yawa daga Najeriya, don jin me zai ce bisa ga korafin da aka dade ana yi game da kamfanonin jigilar alhazan Najeriyar.
"Akwai shirye- shirye da yawa da muka yi ko yaushe mukan kalli matsalolin da muka fuskanta a kowace shekara, zamu zauna mu dubi wadanan matsaloli domin a gyara su, dama matsalolin na rashin isassun jirage ne, kuma a wannan karon muna da su. Insha Allahu za mu yi aikin nan cikin sauki tare da yardara, mu koma ranar da aka kammala, za mu iya dawo da mahajattan nan''
A bana dai mahajattana dubu 76 suka samu nasarar shiga cikin jerin wadanda ke fatan sauke faralli a kasar ta Saudiyya, maimakon dubu 99 da akan tura, saboda zabtare kashi 20 cikin dari na mahajattan da mahukutan kasar Saudiyya suka yi ga kowace kasa. A bin jira da ma fata shine, ganin fara aikin jigilara da za'a fara daga ranar 14 ga watan Satumba mai zuwa.
Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Usman Shehu Usman