Najeriya ta samu zuba jari fiye da kowa a Afirka
April 2, 2013Kwararar da jarring daga kasashen wajen ke ci gaba da yi zuwa ga tattalin arzikin Najeriya da shekaru uku kenan a jere yake ci gaba da karuwa musamman a sashin bankuna, samar da wuta lantarki da man fetir a kasar, fanonin da a yan shekarun nan suke samun karuwar masu rigegen zuba jari a cikinsu, musamman saboda mayar da su a hannun yan kasuwa.
Wannan lamari da ke kara mayar da Najeriyar tamkar wata budurwar da ake rige-rige a kanta a fannin zuba jarin duk kuwa da irin kalubale na rashin isassun kayan aiki da kasar ke fuskanta da ma matsalolin tsaro. Abinda ya sanya ministar kula da ciniki da zuba jari a Najeriyar Dr Olusegun Aganga bayyana cewa akwai fa dalilin da ya sanya faruwar hakan, saboda Najeriya na cikin kasashe biyar da cibiyar zuba jarin kasa da kasa ta bayyana wadanda suka fi daukan hankalin masu zuba jari a duniya.
‘'Yace idan ka duba Najeriya ka kwatanta da sauranm kasashe, za ka ga cewa kasa ce da ke da yanayin da ke samar da bunkasar jarin da ka zuba tare da samun riba. Kashi 75 cikin ɗari na kasashen duniya a yanzu suna da yanayin na koma bayan ribar da ake samu a cikinsu, wannan ya sa muke samun ƙarin jarin da ke shiga kasar a fannoni da dama, don haka muna da kyakyawan yanayi domin ciyar da kasar gaba zuwa mataki da ya kamata ta kasance''.
Duk da irin wannan ci gaban da Najeriyar ke samu a yanzu da bayanai daga hukumar sa ido a kan jarin da ake zubawa a kasashen Afrika ya nuna Najeriya a matsayin wace ke kan gaba da kasashen da dama, domin daga jarin da aka zuba a tattalin arzikin kasar na Dalla bilyan shida a shekara ta 2011 da a yanzu ya karu zuwa Dalla bilyan tara a wannan shekarar, ya sanya kasar zama kan gaba a wannan fani cikin nahiyar Afirka.
To sai dai kalubalen da masana harkokin tattalin arzikin da ci gaban kasa ke ganin na gaban Najeriya shine maida hankalin domin yan kasa su ci moriyar jarring da ke shiga kasar, don gujewa mayar das u gugar yasa, abinda ya sanya Malam Ahmed Rabiu masani a fabnin tattalin arziki da harkar zuba jarri bayyana cewa.
‘'Yace watau saboda rashin samun saita al'amarin wadanda suke rike da hukumomin da y a kamata su tabbatar da an yi dai dai, daga maikatan da mu kanmu yan kasuwa, har yanzu ba'a kamala wannan saitin ba, cin hanci da rashawa da sama da fadi da kudin alumma, da rashin tausawa masu da rashin tunanen matsayin da Najeriya take ciki a lokacin da aka kawo wani abu na sauyi. Kullum ya kamata a sani muna nan milyan 160, amma wadanda suka fahimci inda aka dosa basu wuce milyan biyu ba, wadanda suke zuwa kasashen duniya suke ganin su san al'ammura basu wuce rabin milyan ba, amma in an tashi za'a yi wani abu sai dauko wanda yafi kowane ci gaba a duniya a ce shi za'a yi wannan ba dai dai bane''.
Amma ga Dr Sule Bello na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria da ya kasancce kwarrare a fanin ci gaban kasa da kasa yace dole a koma tsarin da aka baro a shekarun baya, domin ganin tasirin lamarin.
‘'Hanya da za'a bi ba wai da fada ba, bada zage-zage ba, ai ka ga mu muke da iko da kanmu dole, a fita kasashen waje in zamu sayi kaya, mu saya in ba haka ba mu sayi na wani, to an canza wancan tsari tun zamanin mulkin malaka wanda yake ma'adananku ne, amma wasu ne ke amfana.
Karuwar zuba jari a tattalin arzikin Najeriyar dai na zama abinda ke haifar da kyakyawar fata ga makomar kasar da ke da zarattan matasan da suka kosa domin samun ayyukan yi domin zaburara da tattalin arzikin kasar.
Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Usman Shehu Usman