Najeriya ta samu kujera a Kwamitin Sulhu | Siyasa | DW | 18.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya ta samu kujera a Kwamitin Sulhu

A karo na biyar an sake zabar Najeriya a matsayin mamba da ba ta din-din-din ba, a Kwamitin Sulhun na Majalisar Dinkin Duniya, sai dai wasu na ganin kawai zakara ne mai neman suna.

Kwararru da ma al'ummar Najeriya sun fara tofa albarakacin bakinsu dangane da da zaben kasar da aka sake yi a matsayin daya daga cikin kasashen da suka zama wakilan da ba na din-din din ba, a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya. To ko wane tasiri wannan ka iya yi ga matsayin Najeriyar a kasashen duinya?

Samun nasarar da Najeriyar ta yi na kaiwa ga wannan matsayi dai ya biyo bayan kamun kafa da ma lanlami a wajen kasashen nahiyar Afrika da dama, wanda tuni ya sanya mahukuntan Najeriyar tsunduma cikin murna da farin ciki bisa abinda shugaban Najeriyar Good Luck Jonathan ya bayyana a matsayin yabawa ne da irin rawar da kasar ke takawa a siyasar kasashen duniya.

Members of the United Nations Security Council raise their hands as they vote unanimously to approve a resolution eradicating Syria's chemical arsenal during a Security Council meeting during the 68th United Nations General Assembly in New York on September 27, 2013. REUTERS/Keith Bedford (UNITED STATES - Tags: POLITICS TPX IMAGES OF THE DAY)

Babban zauren Kwamitin Sulhu

Zama cikin jerin kasashen da ke da wakilcin da ba na din-din-din ba a Kwamitin Tsaron na Majalisar Dinkin Duniyar da ke ci gaba da zama mai uwa da makarbiya a siyasar duniya na zama abin da ake wa kalon muhimmin ci gaba ne ga Najeriyar, musamman a dai dai lokaci da take ci gaba da kamfe na ganin ta samu kaiwa ga zama cikin kasashen da zasu samu zaunannen wakilci a kwamitin sulhu majalisar. To ko wane tasiri wannan ke da shi ga matsayin Najeriyar? Ambasada Sulaiman Dahiru kwararre ne a fanin dangantakar kasa da kasa da ke Abuja.

Titel: Teilnehmer AU-Sondergipfel Abuja Wer hat das Bild gemacht?: Ubale Musa (DW) Wann wurde das Bild gemacht?: 15.7.2013 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Abuja/Nigeria Bildbeschreibung: Bei welcher Gelegenheit / in welcher Situation wurde das Bild aufgenommen? Wer oder was ist auf dem Bild zu sehen? Teilnehmer des Sondergipfels der Afrikanischen Union (AU) zu HIV/Aids, Tuberkulose und Malaria in Abuja (Nigeria). In der Mitte (mit Hut) Nigerias Präsident Goodluck Jonathan.

Shugabannin Afirka a taronsu a Abuja

Kujerar Najeriya a Kwamitin Tsaro ta jeka na yi ka ce

‘'Shiga wannan wuri bai wuce kawai a ce kasa kaza tana cikin wannan kwamiti ba, amma ba za ta iya canza wani abu ba, tana wajen in aka zo za'a yi maganganu a kan abubuwan da ke faruwa a duniya za'a ji shin menene Najeriya ta fada. Don haka zabe da aka yiwa Najeriya cikin kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya Eh za'a ji batun Najeriya ko ina a cikin duniya amma kuma ba wai wani abu ne zai kawowa Najeriya wai ko kudi ko na biyan bukata ba''.

Najeriya dai ta kasance kasar da ke dawainiya wajen tura sojojinta zuwa kasashe da dama domin aikin wanzar da zaman lafiya wanda majalisar dinkin duniya kan yi la'akari da shi wajen sanya kasashe a kwamitoci masu karfi da muhimmanci irin wadannan.

Sanin yadda 'yan Najeriya kan yi doki a kan matsayi da ma yadda ake kallon kasar a harkokin kasa da kasa irin na Majalisar Dinkin Duniya, ya sanya neman ra'ayin wasu al'ummar kasar a kan samun nasarar sake kutsa kai da Najeriyar ta yi.

Wasu 'yan Najeriyar na ganin abun a yaba ne

‘'Abin alfahari ne tunda akwai wasu kasashen Afrika da roko suke yi don su samu shiga wannan kwamiti, amma tunda mu mun samu ai abin farin ciki ne. Tace Ina ganin wannan ya nuna cewa an gane Najeriya tana taka rawa sosai wajen taimakawa kasashen duniya. Yace ba wai batun samun wakilci a wannan kwamiti bane, amma matsalar ita ce ta yiwu kasashen zasu kalli yadda Najeriya take a cikin kasarta ba wai a majalisar ba''

Najeriyar dai ta sake samun kaiwa ga wannan matsayi ne a dai dai lokacin da take kara kaimi wajen ganin ta samu kujerar din-din-din a Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniyar, ya sanya tambayar ko wannan zai iya taimaka mata a wannan fanin? Ambasada Sulaiman Dahiru ya ce.

‘'Ban yi tsamani zai yi ba, domin ai zaben da ake yi za'a zabi kasashe guda 10 ne a wannan kwamitin sulhun na Majalisar Dinkin Duniya, a mtsayi da ba na din-din-din ba, su hadu da wadannan kasashe biyar da suke da zaunannen wakilci su yi shekaru biyu su tafi. Ko wace nahiya zata kawo nata daga Asiya da Afrika da Turai, kaga ai a da in Najeriya ta yi Magana duk duniya tana sauraronta amma yanzu ba haka ba ne, don haka dole sai mun gyara hallayenmu na rashin dai daito a cikin gida''.

Karo na biyar kenan dai a jere da Najeriyar ta samu zama wakiliya a matsayin da ba na din-din-din ba a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniyar. Abin jira a gani shi ne amfanin da wannan ka iya kawowa ga kasar da ma al'ummarta a fagen siyasar duniya da ke kara daukan sabon salo a tsakanin kasashen da suka ci gaba da ke da karfi da masu tasowar da a kullum suke kukan duniyar fa na zama yanayi ne na kashin dankali babba a kan karami inda na sama ke kara dankwafe na kasa.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin