Najeriya: Rage yawan barace-barace a Borno | Zamantakewa | DW | 21.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Najeriya: Rage yawan barace-barace a Borno

A wani mataki na rage yawan barace-barace da ake samu tsakanin nakasassu a Borno gwamnatin jihar ta dauki nakasassu musamman guragu a aikin shara don tsabtace muhalli a Maiduguri.

Wannan dai shi ne karo na farko da ake daukar nakasassu aikin tsabtace muhalli a jihar ta Borno da ke da dubban nakasassu da ke yin bara domin samun na sawa a bakin salati.
Nakasassun ne dai suka mika takardun neman a daukesu wannan aiki wanda ake ganin na masu lafiya ne kuma hukumomi suka amince su dauke aikin wanda na wucin gadi ne da ake biyansu kudade a duk karshen wata.

Ko menene dalilin wadannan nakasassu guragu na neman aiki irin wadannan ga amsar da daya daga cikinsu da aka tarar yana sharar wanda kuma ya ba da sunansa da Abdula-Rahman Kwankwasiyya ya ba wa wakilinmu na Borno Al-Amin Suleiman Muhammad.

"A halin da muke ciki a nan garin masu kafa ma sun kwace mana sana'armu ta bara shi ya sa mu kuma da yake muna da zuciya ta yin aiki, muka ga hukumomi muka ce don Allah su ba mu aiki ko da na sharar gari ne."

Afrika Müll in Angola (DW/A. Vieira)

Yawancin birane a Afirka na fama da tarin shara a tsakiyar gari

Yayin da wasu ke kallon wannan aikin shara na da hadari ga guragu da yawancinsu ke aiki a kan kekunan guragu wasu da sanda hukumomi sun samar musu da kayayyaki na musamman da za a gane cewa ma'aikata ne ta yadda masu ababan hawa za su kiyaye su.

Hukumar kula da tsabtace muhalli ta ce ta dauki guragun aikin shara don tsabtace muhalli ne da kuma rage musu wahalhalu da suke fuskanta yayin yin barace-barace a manyan hanyoyin birnin Maiduguri. Akasari dai wadannan nakasassun suna aikin share wasu manyan hanyoyi ne da ke cikin garin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno.

Shugabannin kungiyar nakasassu dai sun ce sun ji dadi matuka da aka dauki nakasassu wannan aiki sai dai suna roko a mayar musu da aiki na dindindin maimakon na wucin gadi.

Masharhanta dai sun ce daukar nakasassu wannan aiki zai taimaka musu a rayuwarsu ga kuma ribar tsabta don kare muhalli da al'umma baki daya daga cutukan da ake samu daga rashin tsabta.

Sauti da bidiyo akan labarin