1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar tsaro na iya shafar sahihancin zabe a Najeriya

Uwais Abubakar Idris
July 20, 2018

Wasu kungiyoyin kasa da kasa da ke nazarin harkokin dimukuradiyya, International Democratic Institute sun fitar da hasashensu game da zaben Najeriya na 2019

https://p.dw.com/p/31plT
Nigeria wählt Gouverneure und Regionalparlamente
Wata rumfar zabe a lokacin zaben gwamna a Jihar Lagos a 2015Hoto: Reuters/Penney

Tawagar wadannan kungiyoyin kasa da kasa sun kwashe lokaci mai tsawo suna binciken halin da yanayin siyasar Najeriyar ke ciki da ma irin shirin da ake da shi a yanzu yayin da ya rage watanni bakwai a gudanar da zabe, musamman sun nuna damuwa a kan  yanayin rashin tsaro da ka iya kawo cikas ga zaben na Najeriya.

Nigeria Geld Geldscheine Naira in Lagos
Tasirin kudi a zaben NajeriyaHoto: Getty Images

Karuwar amfani da kudi domin sayen kuri’u da suka ce na iya rikidewa zuwa magudi da ma yadda kafofin sada zumunta ke furta kalamai na batanci a kasar duka matsaloli ne da suke bukatar a dauki mataki a kansu a cewar Mr Jan Surotchak daraktan cibiyar nazarin dimukurdiyya ta IRI.

Ko mecece suke gani mafita daga wadannan matsaloli da suka zayyana ga zaben na Najeriya? Dr Pauline Baker ita ce shugabar gidauniyar samar da zaman lafiya ta kasa da kasa kuma da ita  aka gudanar da wannan nazari.

Nigeria Wahlen 2011 Bild 2
Hoton wasu masu zabe a 2011 a NajeriyaHoto: DW/Gänsler

"Ta ce "duk da kalubalen da ke tattare da wannan batu zaben na 2019 ya samar da kyakkyawar dama ga jam’iyyun siyasa da hukumar zabe su tabbatar da cewa an samu ci gab ata fannin yin sashihin zabe a cikin yanayi na zaman lafiya".

Sun dai ja kunnen jam'iyyun siyasa su guji tilastawa jama’a ‘yan takara a kansu, tare da bukatar bai wa mata da gajiyayu dama. Amma ga ‘yan siyasar Najeriyar irin su Abubakar Muazu na ganin ana samun ci gaba a tsarin yadda ake gudanar da zabubbuka a Najeriya.

Amma ga Dr Christopher Fomunyon babban jami’I mai kula da tsakiya da yammacin Afrika a cibiyar nazarin dimukuradiyya ta IRI ya ce akwai hatsarin da suka hango daga wannan matsala.

Duk da hasashen da suka yi sun bayyana cewa ‘yan Najeriya suna da ammanar hukumar zabe za ta iya gudanar da sahihin zabe a shekara mai zuwa, sai dai sun bukaci kasashen duniya su taimaka wa Najeriya a kan lokaci, su kuma kafofin yada labaru su tabbatar da bada rahotani na gaskiya a kan yakin neman zabe.