Najeriya da Ghana sun cimma daidaito | Labarai | DW | 20.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya da Ghana sun cimma daidaito

Kamfanin mai na NNPC a Najeriya ya ce sun cimma matsaya da Volta River Authority na Ghana kan batun bashi sama da Naira miliyan dubu talatin da uku na iskar gas.

Nigeria National Petroleum Corporation Öl-Industrie Korruption

Kamfanin NNPC Abuja

Kamfanin da ke lura da harkokin albarkatun mai a Najeriya ya bayyana cewa sun cimma daidaito da mahukuntankasar Ghana bayan da a baya kasar ta Najeriya ta yi barazanar cewa za ta tsaida albarkatun iskar gas da take ba wa Ghana wanda ke zama wani bangare na abin da take amfani da shi wajen bada wutar lantarki a kasar.

Kamfanin mai na NNPC a Najeriya ya ce sun cimma matsaya da Volta River Authority kan batun bashi sama da Naira miliyan miliyan dubu talatin da uku. Ohi Alegbe jami'i da ke magana da yawun kamfanin na NNPC a Najeriya ya ce baki dayan bashin da suka biyo mahukuntan na Ghana karkashin yarjejeniyar da suka cimma za a kammala biyan kudin zuwa watan Fabrairu na shekarar 2016.

Wannan yarjejeniya dai an kai ga cimmata ne bayan wani zama da aka yi tsakanin shugaban kamfanin na NNPC Ibe Kachikwu da shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama da ministan makamashin Ghana Kwabena Donkor.