Najeriya: Bukatar Saraki ya ajiye mukami | Siyasa | DW | 09.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya: Bukatar Saraki ya ajiye mukami

Takaddama ta kunno kai a game da bukatar shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Bukola Saraki ya sauka domin fuskantar zargin da ake masa a kotun ma’aikata.

To kugen masu kiran shugaban majalisar dattawan Sanata Bukola Saraki ya sauka daga mukamin nasa domin fuskantar shari'a dai, na ci gaba da kara amo a Tarayyar ta Najeriya, tun bayan hukuncin da kotun koli ta yi, inda ta yi watsi da daukaka karar da ya yi, inda kotun ta ce dole ne ya fuskanci shari'a a kan zargin laifin kin bayyana kadararsa a kotun da'ar ma'aikata ta Abujan.

Kama daga tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya zuwa fitaccen lauyan nan mai kare hakkin dan Adam Femi Falana har zuwa ga wasu ‘yan majalisar dattawan Najeriyar, dukkaninsu na masu kiran Saraki ya sauka domin gudun jan suna da ma darajar majalisar. Sanata Kabiru Marafa na cikin masu wannan kira:

Unabhängigkeitstag in Nigeria 2015

Shugaba Buhari da Saraki

Yace "Ni ina ganin duk wanda ya bai wa Sanata Bukola Saraki shawara ya sauka na cikin babban mai kaunarsa ne domin kuwa tuhumar da yake fusknata a kotu batu ne da ya shafe shi, don haka babu dalilin da zai sa ya bari lamarin ya shafi majalisa. Tun da daewa muke da wannan matsayi kuma zamu ci gaba a kan haka, domin shi ne mafita a gare shi da ma darajar majalisar".

Ra'ayoyin dai sun sha banban a tsakanin ‘yan majlisar dattawan kasar, inda wasu da dama ke ganin neman magana ne kawai ya sanya kawo batun murabus ga wanda zargi kawai ake yi masa, kuma bisa dokokin Najeriya wanda ake zargi matsayinsa shi ne wanda bai aikata laifi ba har sai an tabbatar da haka. Sanata Kabiru Ibrahim Gaya na cikin masu adawa da batun yin murabus din na Saraki.

Nationalversammlung in Abuja, Nigeria

Majalisar Tarayyar Najeriya

Wannan lamari dai tuni ya rarraba kawunan wasu ‘yan majalisar dattawan Najeriyar da tun kafuwarta suka kira kansu da ‘yan Unity Forum da na like minds. Ko a yanzu wane mataki suke shirin dauka su da ke dagewa akan lallai sai ya sauka daga mukaminsa? Sanata Kabiru Marafa ya yi karin haske.

A majalisun dokokin baya da suka gabata dai zargi na aikata ba dai-dai ba da suka haifara da guguwar rigingimun sun kai ga tadiye tsofaffin shugabanni irin su Sanata Chuba Okadigbo da Evans Eweram. Abin jira a gani shine yadda za ta kaya a kotun da'ar maikatan, inda za'a fara shari'ar tuhumar da tuni Sanata Bukola Saraki ya musanta zargin da ake masa na kin bayyana kadararsa a lokacin da yake gwamnan jiharsa ta Kwara a tsakanin 2003 zuwa 2007.

Sauti da bidiyo akan labarin