1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci-gaba a matakan wayar da kai kan cutar HIV

Abdullahi Maidawa Kurgwi MNA/UIU
November 27, 2018

Hukumar da ke yaki da yaduwar cuta mai karya garkuwar jiki HIV a jihar Filato da ke Najeriya, ta ce an samu raguwar jama'a da ke kamuwa da cutar, sakamakon yadda jama'a ke daukar matakan kariya sabanin shekarun baya.

https://p.dw.com/p/390QC
AIDS-Test Westafrika
Hoto: AFP/Getty Images

A wata ganawa da DW ta yi da babban daraktan hukumar kula da yaduwar cutar ta AIDS ko Sida a jihar  Filato, Sunday Markus Koka, ya ce sun kafa cibiyoyin shan magani a yankunan kananan hukumomin jihar, yadda masu dauke da cutar ke samun sauki wajen shan magani da ake ba su a kai a kai. Ya kuma nuna cewar akalla mutane dubu araba'in ne ke karbar maganin, har sun kafa wata kungiya domin taimakekeniyar juna tsakaninsu. 

Mata su ne wadanda ke kan gaba a yawan masu dauke da kwayar cutar a jihar, kana kuma matasa su ne mafiya yawan wadanda ke fama da wannan cuta mai karya garkuwar jiki. 

Babban daraktan ya ce ko da shi ke ana kan ci gaba da bincike amma har ya zuwa yanzu, babu maganin da ke warkar da wannan cuta ta Sida sai dai a samu saukinta.

Kyamar da ake nuna wa masu HIV ta ragu

A bangare guda kuma, babban jami'in da ke wayar da kan al'umma dangane da illar cutar a Filato, Gabriel Gotus, ya ce bincken baya bayan nan ya nuna an fi samun masu kamuwa da cutar ta Sida a birane, kana ya ce yanzu an soma samun saukin yanayi da ake nuna kyama ga masu dauke da kwayoyin cutar, sabanin shekarun baya. 

Nigeria HIV-Aufklärungsplakat
Hoto: DW/M. Bello

Rashin nuna kyamar na zama wani abu da ke taimakawa wajen karfafa wa masu fama da cutar. An samu wayewar kai wanda mutane kan kwana wuri guda, su ci abinci bisa sanin cewar ba za su dauki cutar ba. 

A zantawar da DW ta yi da wata mai dauke da cutar wadda ta nemi a sakaye sunanta, ta sheda mana cewar 'ya'yansu uku da maigidanta kafin a gano tana dauke da cutar, to amma mijinta ya gujeta duk kuwa da cewar shi ma ya kamu da kwayoyin cutar, inda yanzu ya bar ta da dawainiyar gida, da biyan kudin makarantar yara. Ta ce sai ta yi noma suke samun abin da za su ci, duka ranar da ta yi fashi to za su kwana da yunwa.

A zantarwar da DW ta kuma yi da wasu mutane da ke dauke da kwayoyin cutar ta Sida, sun nunar da cewar fargabar da suke yi a baya, yanzu ta ragu, kasancewar suna da yakinin ci gaba da rayuwa muddin ba su kauce wa ka'idar shan magani ba.