1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta daure Mubarak Bala bisa yin sabo

Binta Aliyu Zurmi
April 5, 2022

Wata kotu a Kano da ke Najeriya ta yanke wa Mubarak Bala hukuncin zaman gidan yari na shekaru 24 bisa samunsa da laifin bataci ga addinin musulunci.

https://p.dw.com/p/49VC4
Nigeria Blasphemie Prozess
Hoto: REUTERS

Wata babbar kotu a jihar Kano ta zartas da hukuncin zaman gidan kurkuku na shekaru 24 a kan Mubarak Bala wanda ya yi ridda ya fice daga addinin musulunci bayan da ya amsa tuhume tuhume 18 da a ka yi masa a gaban kotun.

laifukan da aka tuhumi Mubarak Bala da su sun hada da yin kalaman tunziri da tayar da hankulan jama'a da kuma aikata sabo.


Mubarak dai ya amsa cewar ya amince ya aikata dukka laifukan duk kuwa da kokarin da lauyansa ya yi na hana shi amsawa. 

Alkalin kotun justice Faruk Lawan ne ya zartas masa da hukuncin bayan da Mubarak Bala ya amsa cewar ya na sane da sakamakon laifukan da ya aikata.