1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daliban Kagara sun dawo gida

Abdoulaye Mamane Amadou
February 27, 2021

Mahukunta a Najeriya sun ce an sako mutanen nan 42 da aka sace tare da yin garkuwa da su a garin Kagara na jihar Neger, bayan sun shafe tsawon kwanaki 10 suna hannun 'yan bindiga.

https://p.dw.com/p/3q0HW
Symbolbild Entführung Schüler Nigeria
Hoto: Sunday Alamba/picture-alliance/AP

Mutanen da suka hada da daliban makarantar gwamnati da malamansu, sun fada hannun wasu maharan ne da suka yi awon gaba da su. Gwamnan jihar Niger Najeriya ya bayyana a shafinsa na Twitter da cewar an sallamo daliban kana kuma ma har mahukunta sun gana da su. Sai dai sakin daliban na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan bindiga ke ci gaba da garkuwa da wasu daliban makaranta fiye da 300 da suka sace a wata makarantar gwamnati ta Jangebe da ke karamar hukumar Talatar Mafara ta jihar Zamfara, da ke fama da hare-haren 'yan bindiga.