Nadine Gordimer ta mutu | Labarai | DW | 14.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nadine Gordimer ta mutu

Daya bayan daya 'yan gwagwarmayar kasar Afirka ta Kudu da suka yi yaki da mulkin wariyar launin fata na karewa.

'Yar gwagwarmayar yaki da wariyar launin fata kuma shahararriyar marubuciya da ta zama mace guda tilo 'yar Afirka da ta taba lashe kyautar marubutun adabi ta Nobel Nadine Gordimer ta rasu. Gordimer dai ta rasu ne tana da shekaru 90 a duniya.

Gordimer ta taka muhimmiyar rawa wajen kawo karshen mulkin Turawa na wariyar launin fata da aka yi fama da shi a Afirka ta Kudu. 'Yar fafutukar 'yancin bakaken fatar ta yi gwagwarmaya tun lokacin da ake tsare da Nelson Mandela zuwa lokacin da ya samu nasarar darewa kan karagar mulkin kasar a shekarar 1994. A shekara ta 1991 ne Nadine Gordimer ta lashe kyautar marubutun adabi ta Nobel dangane da muhimmiyar rawar da rubuce-rubucenta suka taka wajen ci gaban rayuwar al'umma.

Daga cikin littafan da ta rubuta akwai "A Guest of Honour" da "The Conservationist" da "Burger's Daughter" da "July's People" da kuma "A Sport of Nature". Tuni dai jam'iyya mai mulki a Afirka ta Kudun ta ANC ta bayyana mutuwar ta Gordimer a matsayin babban rashi inda ta bayyana ta da cewa babbar abar koyi ce ga al'umma baki daya.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Suleiman Babayo