An nemi sanya wa sojoji takunkumi
August 5, 2019Talla
Tawagar majalisar da ke gudanar da bincike kan rikicin kabilancin da ya haifar da kisan kiyashi, ta ce ta gano yadda rundunar ke amfani da kafar wajen samun kudin siyan makamai da zummar shafe 'yan kabilar Rohingya daga doron kasa.
'Yan kabilar Rohingya fiye da dubu dari bakwai ne dai, suka tserewa rikicin kasar zuwa Bangladesh a shekarar 2017. Majalisar Dinkin Duniya da sauran kasashen Turai sun ce an aikata kisan kiyashi da yi wa mata fyade a yayin rikicin inda ta dora alhakin kan sojojin gwamnati, lamarin da aka ce ya sabawa dokokin kasa da kasa. Tun bayan fidda sakamakon, gwamnatin Myanmar ba ta ce kalla ba kan wannan zargin.