1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Myammar:MDD ta damu da kisan fararen hula sama da 20

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
March 19, 2024

Rikicin dai ya samo asali ne tun bayan da dakarun kabilu masu gwagwarmaya na Arakan suka farwa sojojin kasar a cikin watan Nuwamban bara, inda sojojin suka ci gaba da kai farmaki Rakhine don murkushe 'yan tawayen

https://p.dw.com/p/4dssy
Hoto: AP Photo/picture alliance

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya nuna matukar damuwarsa kan yadda sojojin Myammar suka hallaka fararen hula sama da 20 a kauyen Rakhine.

Karin bayani:Matasan Myammar sun fara tserewa daga kasar don kaucewa aikin soja na tilas

Wasu mazauna garin ne suka tabbatarwa kamfanin dillancin labaran Faransa APF cewa a ranar Litinin kadai sojojin Myammar sun kashe mutane kimanin 33 da suka hada da mata da kananan yara, sannan kuma suka raunata wasu 10, bayan wasu hare-hare da sojojin saman kasar suka kai yankin.

Karin bayani:An mayar da Myanmar saniyar ware a jerin kasashen kungiyar ASEAN

Rikicin dai ya samo asali ne tun bayan da dakarun kabilu masu gwagwarmaya da makamai na Arakan suka farwa sojojin kasar a cikin watan Nuwamban bara, daga nan ne sojojin suka dauki gabaren ci gaba da kai farmaki kauyukan jihar Rakhine, da nufin murkushe masu tawayen.

Tun a shekarar 2021 ne sojoji suka kwace iko da kasar bayan juyin mulkin da ya hambarar da gwamnatin dimukuradiyya.