1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutuwar karin mutane 21 a rikicin Kwango

December 17, 2013

Ana ci gaba da samun rigingimu a Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango duk da yarjejeniyar tsagaita bude wutar da aka cimma da 'yan tawayen kungiyar M23.

https://p.dw.com/p/1Aaoq
UN Soldaten und kongolesische Soldaten im Kongo
Hoto: Phil Moore/AFP/GettyImages

Rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya da ke Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango ta sanar da gano gawarwakin mutane 21, wadanda suka hadar da na kananan yara bayan wasu rigingimun da suka afku a yankin gabashin kasar. Wasu daga cikin gawarwakin dai alamu na nuna cewar, rataye mutanen ne aka yi har suka mutu, yayin da wasu kuma sun cika ne bayan fyaden da aka yi musu.

Rundunar ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi alkawarin gano wadanda ke da alhakin tafka ta'asar tare da hukuntasu. Kana ta tura karin dakaru zuwa yankin wanda ke lardin Kivu a yankin arewacin kasar. Ya zuwa yanzu dai, Majalisar Dinkin Duniyar ba ta nuna alamar wadanda ake zargi da aikata laifin ba, amma wasu mutane na dora alhalkin kisan a kan wani bangare na 'yan tawayen kasar, wadanda ke nuna adawa da yarjejeniyar zaman lafiyar da masu rikici a kasar suka sanya wa hannu a kasar Uganda.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe