1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutune 18 sun mutu a harin Beni na Kwango

Mouhamadou Awal Balarabe
December 30, 2019

'Yan tawayen ADF da ke dasawa da Yuganda sun kai hari a garin Beni da ke gabashin Jamhuriyar Dimukaradiyya Kwango inda suka kona gidaje da dama tare da salwantar da rayukan mutanen garin.

https://p.dw.com/p/3VWC3
Demokratische Republik Kongo | Überfall auf UN-Lager in Beni
Hoto: picture-alliance/dpa/0AP Photo/A.-H. K. Maliro

Akalla fararen hula goma sha takwas sun rigamu gidan gaskiya a wani harin da kungiyar tawaye ta ADF ta kai a Beni na gabashin Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango. Kantomar gundumar beni Donat Kibwana wanda ya bayar da wannana sanarwa ya ce an kona gidaje da dama yayin wannan harin.

Dama kungiyoyin farar hular sun ja hankali mahukunta kan yiwuwar kai hare-haren sakamakon karuwar 'yan tawaye a yankin gabashin Kwango. Ita dai kungiyar ADF da ke samun goyon baya daga Yuganda ta shafe shekaru 23 tana cin karenta babu babbaka a kasar.

Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Kwango Laftanar Janar Célestin Mbala ya kafa wata rundunar soji a Beni ba tare da kawo karshen hare-hare ba. Tun lokacin da aka fara sumamen soji a ranar 30 ga Oktoba, an kashe fararen hula sama da 200, a cewar kungiyoyin da ke gudanar da ayyukan jin kai a gabshin Kwango.