Mutumin da ya kera bindigar AK47 ya rasu | Labarai | DW | 23.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutumin da ya kera bindigar AK47 ya rasu

Rahotanni daga Rasha na cewar mutumin nan da ya kirkiri bindigar nan samfurin AK 47 Mikhail Kalashnikov, ya rasu a wannan Litinin din ya na da shekaru 94 da haihuwa.

Mr. Kalashinikov ya rasu ne a wani asibiti da ke yankin Jamhuriyar Udmurtia wadda ke karkashin ikon Rasha kamar dai yadda Viktor Chulkov, mai magana da yawun jagoran jamuriyar ya fada, sai dai bai yi karin haske ba game musababbin rasuwarsa amma kuma rahotanni na cewar ya jima a kwance a asibiti.

Shi dai Kalashinikov ya kirkiri wannan bindiga ta AK 47 ce jim kadan bayan kammala yakin duniya na biyu lokacin ya na da shekaru 20 da haihuwa kuma ta kasance bindigar da ta fi kowacce shahara a duniya saboda irin inganci da sauki sarrafawar da ta ke da ita.

Mwallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman