1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashin ya kai wa jirgin kasa hari a Jamus ya je gaban kotu

January 26, 2023

Kotu a Jamus ta ce harin da wani matashi ya kai da wuka a cikin wani jirgin kasa inda ya kashe matasa biyu ba ya da nasaba da ta'addanci .

https://p.dw.com/p/4MkIo
Jirgin da ke jigilar mutane a kasar Jamus kirar SiemensHoto: Siemens AG

An gurfanar da mutumin da ya kai hari da wuka a cikin wani  jirgin kasa a Jamus tare da halaka mutum biyu a gaban kotu. Sai dai kafin gurfanar da mutumin kotu ta ce harin da mutumin ya kai ba ya da nasaba da ta'addanci.

Kakakin kotun Peter Müller-Rakow ya shaida wa kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP cewa,  ana ci gaba da bincike kan sauran dalilai da suka sa matashin mai shekaru 33 da haihuwa ya kai hari a cikin jirgin kasan yayin da yake kan hanyarsa daga Kiel i zuwa Hambourg inda ya daba wa mutane da dama wuka tare da kisan wasu matasa biyu.

Maharin dai wani matashi ne dan asalin yankin Falasdinu kuma ya yi wannan aika-aika ne kwanaki kadan bayan sallamarsa daga gidan kaso inda aka tsare shi bisa aikata laifin jikkata wani mutum bayan ya masa dukan tsiya.