Mutum na bakwai ya mutu da cutar Ebola a Najeriya
September 3, 2014Talla
Ministan kiwon lafiya na Najeriya ya sanar da cewar mutun na bakwai wanda ke ɗauke da cutar Ebola ya mutu a garin Port-Harcourt mai arzikin man fetir da ke a yankin kudancin ƙasar. Mutumin wanda aka killace ana kuma lura da shi bayan mutuwar wani likitan a cikin watan jiya wanda ya yi hulɗa da shi,ya mutu ne a lokacin da hukumomin Najeriyar ke yin shelar cewar waɗanda ke ɗauke da cutar ba su da yawa.
Sauran mutane guda biyar sun mutu a Lagos ne, kuma yawancinsu jami'an kiwon lafiya ne, kawo yanzu sama da mutane dubu ne suka mutu da cutar a ƙasashen Saliyio da Laberiya da Najeriya da kuma Guinea.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman