Mutum fiye da 270 sun mutu a harin Somaliya | Labarai | DW | 16.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutum fiye da 270 sun mutu a harin Somaliya

Ministan yada labarai a kasar Somaliya Abdirahman Osman ya ce alkaluman mamata a sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai a kasar sun haura 270 kana wasu fiye da 300 suka samu raunika.

Sanarwar ministan ta kara da cewa akwai wasu mutane fiye da 300 ke kwance a gadon asibiti sakamakon munmunar harin kunar bakin waken da aka kai a wata unguwa da ke a birnin Mogadishu a ranar Asabar da ta gabata. Gwamnatin Somalia ta daura alhakin harin kan kungiyar al-Shabab duk da cewa babu wata sanarwa daga kungiyar kan harin da ya kasance mafi muni a kasar a yini guda da ya yi sanadiyar rayukan mutane barkatai.

Kasashen duniya da dama sun yi tir da wannan harin a yayin da kungiyar Tarayyar Afirka ta AU ta nemi hadin kan kasashen duniya domin taimakon kasar ta Somaliya a wannan yanayin da ta samu kanta ciki.