1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Direba ya kutsa kai cikin jama'a da mota

Ramatu Garba Baba
March 22, 2019

Mutune bakwai sun mutu yayin da wasu da dama suka sami rauni bayan da wani direba ya kutsa kai cikin jama'a da motaa a Chaina. 'Yan sanda sun yi nasarar harbe direban da aka ce ya kai harin na wannan Jumma'ar da gangan.

https://p.dw.com/p/3FTKt
Hong Kong Krawalle nach Razzia
Hoto: picture-alliance/epa/J. Favre

Lamarin ya auku ne a birnin Zaoyang da ke yankin Hubei na Chaina. Wani hoton faifan bidiyo na na'urar CCTV da mahukuntan kasar suka fitar,  ya nuna yadda mutumin ya kai harin da kuma gawarwakin jama'a da tarkacen motar maharin. An gano yadda maharin ya soma yunkurin kashe matarsa da 'yarsa kafin ya kai wannan harin.

A farkon watan janairun nan ma dai, Chaina ta zartas da hukuncin kisa kan wani mutum da ya halaka mutum 15 bayan da ya kutsa da mota tsakiyar jama'a kafin daga bisani ya bi wasu yana caka musu wuka.