1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bama-bamai sun tashi daga jikin gawa

Ramatu Garba Baba
February 27, 2019

Mutum 17 ne aka tabbatar da mutuwarsu wasu da dama kuma suka sami rauni bayan fashewar wasu bama-bamai da aka dasa a jikin gawar wani manomi da 'yan bindiga suka kashe.

https://p.dw.com/p/3EDfN
Mali Angriff auf G5 Sahel Basis in der Stadt Sevare
Hoto: Getty Images/AFP

An gano yadda bayan kisan wani manomi, 'yan bindiga suka dasa bama-bamai a jikin gawarsa kafin su kai ta gidan mahaifansa. Ba zato ba tsanmani, bama-baman suka tashi a daidai lokacin da jama'a ke tsakiyar jimamin kisan gillar da aka yi wa mutumin. Daga cikin wadanda harin ya rutsa da su har da iyayen mamacin da wasu danginsa. Lamarin ya kasance irinsa na farko da aka taba gani inji wani jami'in tsaron kasar ta Mali.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas, ke ziyarar aiki a kasar ta Mali, Maas ya ce aikin samar da tsaro da rundunar wanzar da zaman lafiya karkashin Majalisar Dinkin Duniya ke yi, aiki ne mai hadarin gaske da ke bukatar juriya, amma ya ce ya zama dole a yaki ta'addanci. Jamus na da akalla sojoji 170 a Mali. Ministan zai kammala ziyarar a ranar Alhamis