Mutane tara sun mutu a bukukuwan Sallah a Ghana | Labarai | DW | 07.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane tara sun mutu a bukukuwan Sallah a Ghana

Bukukuwan karamar Sallah sun haifar da rasuwar mutane tara sakamakon ture-turen da aka fuskanta a filin wasa na unguwar Asawase da ke birnin Kumasi na kasar Ghana.

Mutane tara ne suka mutu da yammacin ranar Laraba a wani filin taro na Asawase da ke karkashin majalisar karamar hukumar Asokore Mampong da ke birnin Kumasi na kasar Ghana, sakamakon ture-ture da aka fuskanta a lokacin da ake gudanar da shagulgulan karamar Sallah ta karshen Azumin watan Ramadan.

Da yake magana kan wannan hargitsi da ya faru, Nurudeen Hamidan da ke a matsayin shugaban karamar hukumar, ya tabbatar da mutuwar mutanen tara, maza shida da mata uku, dukkansu yara matasa. Ga al'ada dai matasa maza da mata dai ne ke haduwa a wannan fili a duk karshen watan Azumin Ramadan domin gudanar da shagulgulan Sallah.