Mutane takwas sun halaka a harin New York | Labarai | DW | 01.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane takwas sun halaka a harin New York

Wani harin ta'addacin da wani mutum ya kai New York na Amirka ya yi sanadin mutuwar mutane da dama bayan da ya afka wa hanyar da masu keke ke bi a gefen kogin Hudson.Tuni dai 'yan sanda suka dirka wa maharin bindiga.

Wani mutum da ya dauko motar haya ya afka wa hanyar da masu keke ke bi a gefen kogin Hudson kusa da wurin tunawa da harin cibiyar kasuwanci ta duniya a New York Amirka a ranar Talata, inda ya halaka mutane takwas da samar da munanan raunuka ga wasu 11, a harin da masu iko a yankin suka bayyana da harin ta'addanci na rashin imani.

Tuni dai 'yan sanda suka dirka wa maharin bindiga a lokacin da ya yi tsalle don fita daga motar dauke da bindigogi na bogi a lokacin da wadanda suka sheda lamarin ke cewa ya fita tare da yin kabbara. Ana dai sa ran bayan fidar da aka yi wa mutumin da yanzu ke cikin rai kwakwai mutu kwakwai zai iya rayuwa.

Wasu jami'ai da basu so a bayyana sunansu ba sun yi tsokaci kan binciken da ake kawo yanzu kan maharin da suka bayyana da cewa dan shekaru 29 ne mai suna Sayfullo Saipov dan asalin Uzbekistan ya kuma shiga Amirka ta hanyar da ta dace a shekarar 2010.