Mutane sun bace a karkashin kasa a Myanmar
December 26, 2015Talla
Da yake magana da kanfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP, daya daga cikin ma'aikatan yankin, ya ce a halin yanzu dai masu aikin ceto sun fara aikin nemo gawarwaki kuma ba za su iya bayar da wani adadi ba a yanzu. A karshen watan Nuwamba ma dai a kalla mutane 100 ne suka rasu a iri-irin wannan hadari na motsawar kasa a wani yanki mai nisa na kasar da ke iyaka da kasar Sin bayan da wani dutsi ya ragargaje bisa wasu gidaje yayin da mutane ke cikin barci a daidai lokacin.