Mutane shida sun hallaka a harin Lebanon | Labarai | DW | 27.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane shida sun hallaka a harin Lebanon

Harin bam da mota ya hallaka tsohon Ministan Kudin kasar Lebanon da wasu mutanen biyar

Wani hari da mota shake da bama-bamai a tsakiyar Beirut babban birnin kasar Lebenon, ya yi sanadiyar hallaka tsohon ministan kudin kasar Mohammad Chatah, da kuma wasu mutanen biyar.

Rahotannin sun ce harin ya jikata wasu mutanen fiye da 50. Tsohon ministan Chatah ya kasance mai alaka ta kut-da-kut da tsohon Firamnista Saad Hariri, kuma mai adawa da gwamnatin kasar Siriya. Tsohon ministan yana cikin jiga-jigan 'yan adawa na kasar ta Lebanon, kuma dan Sunni wanda yake adawa da kungiyar Hezbollah.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu