1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane na barin gidajensu a arewacin Mali

Salissou Boukari
September 8, 2018

Wata sanarwar kungiyoyin agaji masu aiki a yankin arewacin Mali ta ce tashe-tashen hankula da ake fuskanta na ci gaba da haddasa kwararar mutane da dama da ke yin gudun hijira suna barin matsugunansu.

https://p.dw.com/p/34WXi
Tuareg NMLA - Kämpfer im Norden von Mali
Hoto: picture-alliance/dpa

Kungiyar agaji ta kasar Norwai da ke ayyukan agaji a yankin Menaka na arewacin kasar ta Mali ta sanar da wannan labari, inda ta ce tashe-tashen hankulan da suka hada da rikici tsakanin kabilu, da hare-haren 'yan bindiga, da kuma yawaitar kai samame da sojoji ke yi a yankin tsakiya da kuma arewacin kasar ta Mali, sun haddasa ficewar mutane kusan dubu 50 tun daga watan Janairu kawo yanzu, wanda hakan ke nuni da cewa an samu karuwar masu gudun hijira da kashi 60 cikin 100 idan aka kwantanta da na shekarar da ta gabata a daidai wannan lokaci.

A wata ziyara da ya kai a yankin na Menaka yankin da ya fi ko'ina tashe-tashen hankula a arewacin kasar ta Mali, Patrick Youssef, da ke a matsayin babban jami'in kungiyar agaji ta kasa da kasa ta Red Cross, ya yi kira ga masu dauke da makammai da su dubi mutuncin fararen hula tare da bada dama ga masu ayyukan agaji.