1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin aikin yi na karuwa a duniya

Abdullahi Tanko Bala
January 21, 2020

Miliyoyin ma'aikata a fadin duniya suna rayuwa hannu baka hannu kwarya yayin da a waje guda rashin aikin yi ke karuwa.

https://p.dw.com/p/3WXJ2
Bangladesch Dhaka Gerberei
Hoto: bdnews24/A. Al Momin

Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar tare da tallafin kungiyar kwadago ta duniya ILO yace mutane kimanin miliyan 500 a fadin duniya basu da aiki nagartacce ko kuma basu ma da aikin yi.

Rahoton yace an sami dan daidaiton rashin aiki a shekarar 2010 sai dai kuma ana kyautata tsammanin rashin aiki zai karu zuwa mutane miliyan biyu da rabi a wannan shekarar ta 2020.

Shugaban kungiyar kwadago ta duniya Guy Ryder yace miliyoyin ma'aikata a duniya suna rayuwa hannu baka hannu kwarya. Adadin marasa aikin su miliyan 470 a fadin duniya daidai yake da kwatankwacin kashi 13 cikin dari na daukacin ma'aikata a duniya baki daya.