1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane fiye da milliyan 50 na gudun hijira

June 20, 2014

Hukumar kula da 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan mutane miliyan 17 sun bar kasashensu, fiye da mutane miliyan 33 kuma na cikin kasashensu

https://p.dw.com/p/1CNJU
DW_Mali_Flüchtlinge 2
Hoto: DW/K. Gänsler

A karon farko tun bayan yakin duniya na biyu, adadin mutanen da aka tilastawa barin matsugunnensu ya wuce milliyan 50, a cewar Hukmar kula da 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya.

'Yan Siriyan da ke gudu daga yakin basasar da ke cigaba da daidaita 'yan kasa, dama sauran rikice-rikice daga sassan duniya daban-daban, suka janyo karuwar wannan adadi, kamar dai yadda hukumar ta bayyana a cikin wani rahoton da ta wallafa mai suna Global Trends Report a turance.

Kwamishanan wannan hukuma Antonio Gueterrs wanda ya gabatar da wannan rahoton ya ce a karshen shekarar da ta gabata mutane millyan 51 da digo biyo ne aka tilastawa barin gidajensu na ainihi, kuma wannan adadi ya wuce na bara wancan da kimanin milliyan shidda, abin da a cewar hukumar, ya nuna gazawa wajen dakile rigingimun da suka dade da ma yin rigakafin barkewar sabbin rigingimu.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Usman Shehu Usman