1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane da dama sun halaka bayan wata gobara a Pilipin

Yusuf BalaMay 14, 2015

Wasu rahotanni na cewa mutane 200 ne ke aiki a wannan masana'anta da ake haɗa takalma, inda tuni sama da mutane saba'in suka hallaka cikin ma'aikatan.

https://p.dw.com/p/1FPkP
Mindestens 72 Tote nach Feuer in Schuhfabrik auf Philippinen
Hoto: Reuters/E. De Castro

Ana ci gaba da samu ƙaruwar addadin mutane da suka hallaka sakamakon wani bala'in gobara da ya afka wa wata ma'aikatar sarrafa talkallama a ƙasar Pilipin, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 72 a dai dai lokacin da ma'aikatan kashe gobara ke ƙoƙari wajen gudanar da aiyyukan ceto a wannan ginin masana'anta, kamar yadda minista a ma'aikatar harkokin cikin gida na ƙasar ya bayyana.

Minista Manuel Roxas a lokacin da ya ziyarci inda lamarin ya afku yankin Manila da ke wajen birnin Valenzuela ya bayyana afkuwar haɗarin a matsayin abu mai muni inda ya ce ba wa iyalan waɗanada abin ya rutsa da su tabbacin cewa za a gudanar da bincike sannan a gurfanar da waɗanda suka zama musabbabin afkuwar haɗarin.

Babu dai tabbaci kan mutane nawa ne cikin ginin masana'antar mai hawa biyu kasancewar littafin da ke ɗauke rubutun sunaye na ma'aikata da suka je wajen aiki ya ƙone. Sai dai wasu rahotanni na cewar mutane 200 ne ke aiki a wannan masana'anta.