Mutane da 10 sun hallaka a Pilipin | Labarai | DW | 02.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane da 10 sun hallaka a Pilipin

Wasu abubuwa masu fashewa da kawo yanzu ba a kai ga tantance su ba, sun tarwatse a cikin kasuwa a birnin Davao da ke kasar Pilipin.

Jami'an tsaron Pilipin sun killace kasuwa a birnin Davao, bayan fashewar wasu abubuwa.

Jami'an tsaron Pilipin sun killace kasuwa a birnin Davao, bayan fashewar wasu abubuwa.

Birnin na Davao da ke kudancin kasar ta Pilipin dai, na zaman mahaifar shugaban kasar Rodrigo Duterte. Rahotanni sun nunar da cewa kawo yanzu mutane 10 ne aka tabbatar sun hallaka yayin da wasu 60 suka jikkata sakamakon fashewar abubuwan da kawo yanzu ba a tantance ko menene da ma dalilin faashewar tasu ba. A tabakin kakakin gwamnatin kasar ta Pilipin Ernesto Abella abubuwan fashewar sun tarwatse ne a yayin cin kasuwar dare, kana Shugaba Duterte na birnin na Davao yayin da abubuwan suka faashe, sai dai babu abin da ya same shi.