Habasha: Mutane 67 sun mutu a zanga-zanga
October 25, 2019Talla
Shugaban 'yan sanda na yankin Oromiya Kefyalew Tefera ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa daga cikin mutanen 67 da suka rasu 55 fararen hula ne yayin da ragowar kuma jami'an tsaro ne.
Takaddama ta kunno kai a kasar ta Habasha sakamakon rashin jituwa tsakanin Firaminista Abiy Ahmed da tsohon na hannun damansa Jawar Mohammed da suka yi hannun riga da kuma rashin gamsuwa da wasu mutanen Oromiya suke nunawa game da salon mulkin gwamnatin Abiy Ahmed wanda shima dan yankin Oromiya ne.
Sabon rikicin dai na iya jefar kasar ta Habasha wadda ke fama da rigingimun kabilanci cikin wani wadi na tsaka mai wuya.