Mutane 17 suka mutu a gobarar Landan | Labarai | DW | 15.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 17 suka mutu a gobarar Landan

Masu aikin ceto a birnin Landan na can na ci gaba da kokarin nemam mutane da suka yi batan dabo, a cikin benen da ya yi gobara a daran Larba.

Shugaban jami'an aikin kwana-kwana na Landan Dany Cotton ya ce da wuya a samu wadanda ke da sauran shan ruwa a gaba a cikin yanayin da wutar take kara ruruwa ga kuma tsananin zafi. Wasu kafofin yada labarai sun ambato gomai na iyalai da suka bace wadanda har ya zuwa yanzu ba a ji duriyar su ba. Ko da shi ke ya zuwa yanzu ba  san dalilan tashin gobarar ba, amma dai ,jama'ar da ke zaune a soron  benen na yn korafin a game da rashin tsari wajen tafiyar da ayyuka samar da lantarki a benen.