Mutane 16 sun rasa ransu a Iraki
April 12, 2018Talla
Salaheddin Shaalan magajin garin Sharqat, ya shaidawa manema labarai cewa mutane 14 na kwance a asibiti cikin mawuyacin hali sakamakon harin da aka kai a makabartar. Kasar ta Iraki dai ta jima tana fama da hare-haren ta'addanci daga kungiyar mayakan na IS da suka addabi kasashen Irakin da Siriya, kana suke neman zama annoba a duniya baki daya.