1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenaya: An kashe dukkan maharan Nairobi

Mohammad Nasiru Awal
January 16, 2019

Shugaba Uhuru Kenyatta ya sanar da cewa dakarun tsaron kasar sun kashe dukkan 'yan ta’adda su hudu da suka kai hari kan wani kasaitaccen otel da rukunin ofisoshi a Nairobi babban birnin kasar a ranar Talata.

https://p.dw.com/p/3BepW
Kenia Angriff auf Hotel in Nairobi
Hoto: Reuters/N. Mwangi

Akalla fararen hula 14 suka mutu sakamakon harin yayin da aka yi nasarar kwashe mutum 700 zuwa tudun mun tsira a cewar Shugaba Kenyatta. 

A jawabin da ya yi ta gidan talabijin na sanar da kawo karshen aikin tabbatar da tsaro a otel din "dusitD2" da ke birnin Nairobi, Shugaba Uhuru Kenyatta bai tantace yawan mutanen da suka kai harin ba amma ya ce dakarun tsaro sunn kashe 'yan ta'adda hudu da suka kai harin, sannan wadanda ba su ji ba su gani ba fararen hula 14 da suka hada da 'yan kasar ta Kenya 11 da dan Birtaniya daya da kuma Ba-Amirke daya na daga cikin wadanda harin ya yi ajalinsu. Sai dai wasu rahotanni na cewa adadin ya zarta haka.

Ya ce: "Ina mai tabbatar cewa an shawo kan lamarin a cikin otel din dusitD2 an kuma kawar da dukkan 'yan ta'addan. Ya zuwa yanzu mun tabbatar da mutuwar mutane 14 sannan da dama sun jikkata a harin da 'yan ta'addan suka kai. Kasarmu gaba daya tana cikin makoki."

Shugaba Kenyatta ya yi kira ga 'yan kasar da su koma bakin aikinsu ba tare da fargaba ba yana mai cewa akwai tsaro a kasar da ke yankin gabashin Afirka. Sai dai a wannan safiya ta Laraba ma an jiwo karar harbe harbe a kusa da otel din.

Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya
Shugaba Uhuru Kenyatta na KenyaHoto: imago/i Images

Al'ummar Kenya dai sun yi kira ga gwamnati da ta karfafa matakan tsaro sannan ta yi duk iyawarta don hana sake kai harin ta'addanci a kasar. Florence Nafula da ke birnin Nairobi ta ce suna cikin fargaba.

Ta ce: "Muna cikin fargaba, ina harkata ta kasuwanci sai na ji wannan abu ya faru, ina cikin fargaba sosai. Muna kira ga gwamnati da ta shawo kan matsalar rashin tsaro. Laifin jami'an tsaro ne na cikin gida domin me ya sa har 'yan ta'adda za su shigo kasar nan duk da matakan tsaron da muke da su."

A halin da ake ciki 'yan uwan wadanda harin ya rutsa da su sun yi cincirindo a gaban asibitoci a birnin Nairobi don tantance 'yan uwansu. Mohamed Yasin Jama dan asalin Somaliya mazaunin birni Nairobi da ya ce hotunan da aka watsa ta kafafan sada zumunta sun taimaka wajen gano gawar daya daga cikin abokan aikinsu.