Kwango: Hadarin jiragen kasa ya halaka mutane 13
July 1, 2019
A Jamhuriyar Dimukudiyar Kongo mutane 13 sun gamu da ajalinsu sakamakon wani hadarin jiragen kasa da ya auku a daren Lahadi wayewar wannan Litinin. Hadarin ya auku ne a kusa da Pointe-Noire da ke kudancin kasar bayan da jiragen kasar 2 shake da kaya sukayi karo da junansu.
Majiyoyi daga cibiyar kula da zirga-zirgar jaragen kasa cewa da CFCO su labarta cewa daya daga jiragen ya samu matsalar naura ne lamarin da ya kai shi yin cikin daya jirgin dake kan hanyar sa. Hukumar 'yan sandar Kongo ta tabbatar da aukuwar hadarin wanda ya lakume rayukan mutane 13 wadanda galibi pasinjoji ne.
Ba bakon abu ne ba dai samun hadarin jiragen kasa a wannan yanki na Jamhuriyar Dimukudiyyar Kwango domin ko da a shekarar 2010 wani hadari makamancin wannan ya ristsa da rayukan mutane fiye da 50.