Mutane 12 sun mutu a taron addini a kasar Portugal | Labarai | DW | 15.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 12 sun mutu a taron addini a kasar Portugal

Mahukunta a Portugal sun tabbatar da mutuwar mutane 12 bayan da wata tsohuwar bishiya ta fada a kan jama'ar da ke taron addini a yankin tsibirin Madeira na kasar.

Mabiya addinin Krista na tsakiyar ibada a lokacin da bishiyar ta fada a kansu. Baya ga wadanda suka mutu akwai kuma mutane fiye da hamsin da suka sami rauni a cewar hukumomin kasar ta Portugal.

Hotunan bidiyon da kafar talabijin a kasar ta yada ya nuna yadda masu aikin agajin gaggawa ke gudanar da aikin ceto rayukan mutane tare da bai wa wadanda suka ji rauni kulawa. Al'amarin na wannan Talata ya matukar tayar da hankulan jama'ar kasar. Ana dai ganin alkaluman mamatan zai iya haurawa nan gaba.