Musulmin Indunusiya na sallah da fargaba | Labarai | DW | 17.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Musulmin Indunusiya na sallah da fargaba

Jiragen sama na kasar Indunusiya dauke da fasinjoji masu son zuwa bikin sallah na fuskantar kalubale a filayen jirgin sama saboda aman wutar duwatsu.

Indonesien Lesende Muslima

Wasu musulmin kasar Indonesiya na karatun Kur'ani

Wasu manyan tsaunuka da suka yi aman wuta a jiya Alhamis a kasar Indunusiya sun sanya an rufe filin tashi da saukar jiragen sama uku ciki kuwa har da filin da birni na biyu mafi girma a kasar ke amfani da shi.

Tsaunin Raung da ke a tsibirin Java ya yi bindiga tare da watsa toka da baraguzai zuwa sararin samaniya da nisan mita 2,000 bayan rugugi da ya dauki makwanni ya na yi. Haka nan ma tsaunin Gamalama a gabashin kasar ta Indunisiya shi ma ya yi aman wutar a jiya Alhamis bayan shiru na watanni.

Wannan rufe filayen tashi da saukar jiragen sama na zuwa ne a daidai lokacin da al'ummar wannan kasa da ke zaune a wasu kasashen waje, ke tudada kasarsu ta haihuwa dan halartar bukukuwan Sallah bayan ibadar azumin watan Ramadana a wannan kasa da ke zama fitacciya da yawan Musulmi a duniya.