Musulmin duniya na gudanar da bikin Sallah layya | Labarai | DW | 04.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Musulmin duniya na gudanar da bikin Sallah layya

A birnin Kano sabon sarki Muhammad Sanusi na biyu ya yi hawan Sallah duk kuwa da rashin tsaron da ake fama da shi wanda a baya ya ragewa Sallah armashi.

Sama da mutane miliyan biyu ne da ke yin aikin hajji a ƙasa mai tsarki ta Saudiyya.Suka fara aikin ibada na jiffar sheɗan a garin Mina da ke kusa da Makka a yau ranar da musulmin duniya ke gudanar da bukukwan Sallah layya.

Aikin ibadar na jiffar sheɗan na ɗaya daga cikin manyan aiyyukan da suka zama wajibi ga mahajjatan bayan tsayuwar Arfa wacce aka yi a jiya. Wakilin DW a Makka Abdullahi Maidawa Kurgwi ya ce a bana ana gudanar da ibadar cikin wani yanayi na zafin rana mai tsananin gaske.