Musayar harbe-harbe a gabashin Kongo | Labarai | DW | 27.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Musayar harbe-harbe a gabashin Kongo

'Yan tawayen M23 sun sake buɗe wuta a kan dakarun Kongo da ke samun tallafin ƙasashen duniya.

'Yan tawayen M23 sun sake ƙaddamar da hare-hare a kan dakarun Kongo, da ke wajen garin Goma, a yankin gabashin ƙasar. A cewar Olivier Hamuli, kakakin rundunar soji a yankin arewacin Kivu, tun a wannan Litinin ce,ɓangarorin biyu suka fara musayar wuta a yankin Kibati, mai tazarar kilomita 20 daga arewacin garin Goma, da ke zama babban birnin lardin arewacin Kivu. Jami'in sojin ya fadi ta tashar rediyon Okapi, da ke ƙasar cewar, a shirye sojojin suke su ɗauki fansa a duk lokacin da 'yan tawayen suka yi yunƙurin nausawa gaba. Tun a ranar Larabar da ta gabata ce, dakarun Kongo, waɗanda ke samun tallafin rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya a Kongo, ke fafatawa da 'yan tawayen M23, waɗanda ke sabunta hare-haren da suke kai wa.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Abdourahamane Hassane