Musayar Fursunoni | Labarai | DW | 09.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Musayar Fursunoni

An tabbatar da Musayar 'yan leƙen asiri tsakanin Rasha da Amirka, a wani matakin kaucewa ɓaraka tsakanin ƙasashen biyu

default

Barack Obama da Dmitry Medvedev

Rasha da Amirka sun fara musayar Fursunoni masu leƙen asiri mafi girma tun kawo ƙarshen yaƙin cacar baka. Wani jirgin sama ya koma da  Rashawa goma da aka zarga da yin leƙin asiri a ƙasar Amirka bayan da aka gabatar da su a kotu inda suka amsa aikata laifin. Ita ma Rasha ta saki Amirkawa huɗu da a da aka ɗaure don zargin yin leƙen asiri, ama suka samu afuwar shugaban ƙasa, bayan da suka amasa a rubuce laifin da ake zarginsu da aikatawa. Wannan musayar fursunonin dai  an aiwatar da ita cikin gaggawa, a wani abinda masana ke ganin wani mataki ne na kaucewa dagulewar dangataka tsakanin Rasha da Amirka .

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Halima Balaraba Abbas