Murna ta koma ciki ga makiyaya a Somaliya da Habasha | Duka rahotanni | DW | 17.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Murna ta koma ciki ga makiyaya a Somaliya da Habasha

Kokari da burin makiyay a Somaliya da Habasha na watanni shida na samun ruwan sama da ciyawa ga dabbobinsu ya ci tura, kuma barazana babba ga dabbobinsu da ma tsarin rayuwarsu.

Takaicin makiyayi

“Abun damuwa ne kwarai, har yanzu ina kokarin kwantar wa da kaina hankali a cewar Mohammed Noor mai shekaru 40. Kamar sauran makiyayan Habasha a yankin Somaliya, ya yi tafiyar daruruwan kilomita zuwa gabar ruwan Somaliland bayan samun labarin ruwan sama da ciyawa mai kyau. Amma babu ruwan da yawa, ba zai ishi dabbobin ba. Yanzu  Awaki 30 ne kacal suka rage daga cikin 100 da Mohammed ya mallka. Rakuminsa daya ya mutu biyu kuma sun rayu."