Murkushe harin ta′addanci a Venezuwela | Labarai | DW | 07.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Murkushe harin ta'addanci a Venezuwela

Mahukuntan Venezuwela sun sanar da cewa sojojin gwamnati sun yi nasarar murkushe wani yinkurin harin ta'addanci da wasu 'ya ta'adda suka so su kai a wani barikin sojin kasar.

Shugaban kasar Nicolas Maduro ne ya sanar da hakan a wani jawabi da ya gabatar a jiya Lahadi a gidan talabijin na gwamnatin kasar inda ya ce wasu mutane kimanin 20 suka kai harin tun da sanyin safiyar jiya Lahadi a barikin sojojin na garin Valencia da ke da nisan kilomita 180 yamma da birnin Caracas. 

Shugaba Nicolas Maduro ya kuma bayyana cewa sojojin gwamnati sun yi nasarar halaka biyu kana suka kama wasu takwas daga cikin maharan bayan da musayar wuta ta sama da awoyi uku. Shugaban ya ce za a gurfanar da mutanen a gaban kuliya inda ya kara da cewar "na bukaci kotu ta yanke hukunci mai tsanani kan duk mutanen da aka samu da hannu a cikin kitsa kai harin ta'addanci."

Tuni dai mahukuntan kasar ta Venezuwela suka zargi kasar Amirka da kitsa wannan hari bayan da a cewarsu wasu daga cikin maharan da aka kama da suka hada da wasu manyan sojojin kasar da suka gudu daga bakin aiki suka tabbatar masu da hakan a lokacin tatsar bayanai.