'Mun karbe ikon gudanar da shari'ar zabe daga kotuna'
September 28, 2024Matakin 'yan majalisar na zuwa ne gabanin babban zaben shugaban kasar da za a gudanar a kasa da kwanaki 10. 'Yan majalisa 116 daga cikin 161 ne suka kada kuri'ar ragewa bangaren shari'a ikon yanke hukunci kan zabe.
ME AL'UMMA YA KAMATA SU SANI GAME DA DOKAR?
Dokar dai ta dakatar da alkalan kotun kundin tsarin mulkin kasar daga gudanar da shari'un da suka shafi zabe, baya ga korar alkalan kotun kolin kasar da shugaba Kais Saied ya yi a shekara ta 2022, bayan takun sakar da ke tsakanin bangaren shari'ar da kuma hukumar zaben kasar, wanda shugaba Saied ne ya nada mambobinta.
Karin bayani: Fushin matasa na kara tsananta gabanin zabe a Tunisiya
Tun dai 'yan adawa da kungiyoyin farar hula suka kira gangamin nuna adawa da matakin 'yan majalisar dokokin kasar.