Mummunan hari kan dakarun MDD | Labarai | DW | 09.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mummunan hari kan dakarun MDD

Akalla dakarun kiyaye zaman lafiya 15 aka hallaka yayin da wasu 53 suka jikkata a Kwango bayan harin ba za ta da aka kai musu

An kai daya daga cikin hari mafi muni ga dakarun kiyaye zaman lafgiya na MDD. Harin da aka kai wa rundunar ta MDD da ke aiki a kasar Kwango ya yi sanadiyyar mutuwar dakaru 15, abin da ya sa harin ya kasance daya daga cikin mafi girma a tarihin aikin wanzar da zaman lafiya na MDD. Sojoji 15 da suka mutu dai an bayyana cewar 'yan kasar Tanzaniya ne, yayin da wasu kimanin 53 suka mutu, a wani abin da aka kwatanta a matsayin daya daga cikin hari mafi muni a tarihin ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD. Tun shekara ta 1999 ne dai aka tura rundunar kiyaye zaman lafiya a kasar Kwango.